Posts

Showing posts from March, 2019

[[Tausayi]] TAUSAYIN SAYYIDINA USMAN (R) GA TALAKAWAN MADINA!

Image
A wata shekara aka yi wani mummunan fari, abinci ya yi matukar wahala ga mutanen Madina. Ko da kuɗi sai an sha wahala kafin a samu abinda za'a ci.

Ana cikin wannan yanayi, tsanani ya yi tsanani, kwatsam sai ga wasu raƙumma kimanin guda dari ko fiye da haka sun iso Madina daga ƙasar Sham (Syria) ɗauke da lodin kayan abinci da hatsi masu yawan gaske, kuma duk mallakin Sayyidina Usmanu dan Affan ne (RA).

Koda zuwan waɗannan raƙuma, sai 'yan kasuwa da yawa suka zagaye Sayyidina Usmanu suna so su saya waɗannan kaya. Sai ya tambaye su wacce riba zasu ba shi? Suka ce za su ba shi riba kashi biyar bisa ɗari. Ya ce, a'a, ai akwai wanda zai bashi fiye da haka.

Sai suka yi mamaki, wane ne wanda zai iya ɗora masa akan yadda suka taya? Su dai basu san wani ɗan kasuwa ba wanda zai iya ƙara masa akan haka ba.

Sai yace dasu, "Ni kuwa na san wani wanda zai bani riba linki ɗari bakwai akan kowanne dirhami guda!" Sai ya karanta masu wata aya daga cikin Qur'ani wadda Allah Maɗau…

[[Cigaba]] FASSARAN LITTAFIN HUQBATUN MINAT TARIKH RUBUTU NA 15

Image
Cigaba Da Fassarar Littafin (حقبة من التاريخ)

Rubutu Na 014

Idan Ba'a Mantaba Har Yanzu Dai Muna Cikin Bayani Akan Khalifanci Abubakar (R) Wanda A Wancan Satin Da Ya Gabata Mun Tsayane A Shafi Na 48 Wanda Yanzu Kuma Insha Allahu Zamu 'Dora Zuwa Shafi Na 49.

MALAM YACE:

●Banu Hanifa Da Yaqin Yamama:

Abubakar (R) Ya Aika Khalid Bn Waleed Domin Yaqar Banu Hanifata, Haqiqa Abubakar (R) Gabanin Haka Ya Aika Ikhramatu Bn Abiy Jahal, Da Kuma Sharahbil Bn Hassanatu, Rundunar Abu Hanifa Sun Kasance Yawansu Yakai Kimanin Dubu Arb'ain ( 40,000 ) Da Khalid Yaje Sai Ya Sanya Sharahbil Shine Na Gaba Na Dama Shine Zaid Bnul Khaddab Da Al-Maisarata Abaa Huzaifata.

Musulmai Sukayi Gaba, Har Khalid Ya Sauka Da Su Kan Wani Tudun Yashi, Yana Ganin Garin Yamama, Kamar Yana Gani, Sai Ya Kafa Rundunarsa, Tutar Muhajirai Tana Tare Da Salim Bawan Abu Huzaifata, Tutar Mutanan Madina Tana Wajen Thabit Bn Qaiys, Yaqi Yayi Tsanani, Har Thabit Ya Haqawa Diddigensa Rami Izuwa Rabin Kwaurinsa, Bayan Yasa…

[[Labarai]] CP WAKILI YA KAIWA SHUGABAN IZALAN KANO ZIYARA!

Image
CP MUHAMMAD WAKILI YA KAIWA SHUGABAN IZALA NA JIHAR KANO ZIYARA.

A yau Asabar, 16-3-2019 ne, Kwamishinan ÿan Sanda na Jihar Kano Muhammad wakili ya kai ziyarar ga shugaban Kungiyar Izala na jihar Kano, Dr. Abdullahi Saleh Pakistan.

CP wakili, ya kai wannan ziyara ne domin girmamawa da kuma samun kwarin gwiwa a ayyukan da yake gabatarwa a wannan jiha tamu mai albarka.

A yayin ziyayar, Dr. Abdullahi Saleh Pakistan ne ya fara gabatar da jawabai na nasiha da jan hankali ga Cp wakili akan ya rike aikinsa hannu biyu-biyu, kuma yasan cewa Allah zai tambayeshi akan dukkan abinda ya gabatar.

" ka sani cewar dukkan aikin da mutum yakeyi, zai iya wakiltar musulunci a wajen, kayi iyaka kokarinka wajen kare musulinci da aikin da kakeyi. Kuma kayi Adalci a aikinka, domin Allah zai tsayar dakai yayi maka hisabi a kiyama...''
- Inji Dr. Pakistan

Dr. Abdulmudallib Muhammad, shima ya dora da nasiha ga CP wakilin, duk dai don fita hakkin shari'a akansa.

Shima a nasa bangaren, Cp Wakili …

[[Cigaba]] FASSARAN LITTAFIN HUQBATUN MINAT TARIKH RUBUTU NA 13B

Image
Cigaba Da Fassarar Littafin (حقبة من التاريخ)

Rubutu Na 013B

Sayyidina Abubakar (R) yaci gaba da cewa:

Babu Wanda Za A Kar6i Wani Aiki Nasa A Wannan Duniya Har Sai Ya Yarda Da Shi (Abin Da Annabi Ya Zo Da Shi)  Wanda Duk Bai Yarda Da Shi Ba To Baza'a Kar6i Aikinsa A Lahira Ba Komai Da Komai. Haqiqa Labari Ya Riskeni Cewa Wasu Daga Cikinku Sun Bar Addininsu Bayan Ada Sun Shiga Musulunci, Kuma Sunyi Aiki Da Shi, Sunbi Al'amarin Allah Sun Kuma Jahilci Yadda Yake, Ko Sun Amsa Kiran Shedan Ne.

Kuma Allah Ta'alah Yace: "Kuma A Lõkacin Da Muka Ce Wa Malãiku, "Ku Yi Sujada Ga Ãdamu." Sai Suka Yi Sujada Fãce Iblĩsa, Yã Kasance Daga Aljannu Sai Ya Yi Fãsiƙanci Ga Barin Umurnin Ubangijinsa, To Fa, Ashe, Kunã Riƙon Sa, Shi Da Zũriyarsa, Su Zama Majiɓinta Baicin Ni, Alhãli Kuwa Su Maƙiya Ne A Gare Ku? Tir Da Ya Zama Musanya Ga azzãlumai.
[Surat Al-Kahf 50]

Yã kũ mutãne! Lalle Wa'adin Allah Gaskiya Ne, Sabõda Haka Kada Rãyuwar Dũniya Ta Rũɗar Da Ku, Kuma Kada Marũɗi Y…

[[Cigaba]] FASSARAN LITTAFIN HUQBATUN MINAT TARIKH RUBUTU NA 13A

Image
Cigaba Da Fassarar Littafin (حقبة من التاريخ)

Rubutu Na 013A
A Wancan Rubutun Da Ya Gabata Idan Ba'a Mantaba Mun Tsayane A Shafi Na 44 Yanzu Kuma Zamu 'Dora Zuwa Shafi Na 46 Idan Allah Ya Amince.

MALAM YACE:

"Abubakar Ya Koma Garin Madina, Ya Kuma Rubutawa Ko Wacce Tawaga Wasiqa, Ga Kuma Nau'in Wasiqar:

Daga Abubakar Khalifan Manzon Allah (S) Zuwa Duk Wanda Saqon Ya Riskeshi, Gamagarin Mutane Da Shuwagabanninsu, Wanda Ya Tsaya Ga Musuluncin, Ko Wanda Ya Barshi, Amincin Allah Ya Tabbata Ga Wanda Ya Bi Shari'a, Bai Kuma Juyaba Bayan Shiriya Zuwa Ga 6ata Ba, Ni Ina Godiya Ga Allah Gareku Wanda Babu Abin Bautawa Da Gaskiya Sai Shi, Ina Shaidawa Babu Abin Bauta Bisa Cancanta Da Gaskiya Sai Allah Shi Kadaine Bashi Da Abokin Tarayya, Kuma Annabi Muhammad Bawansane Kuma Manzonsa Ne Muna Tabbatar Da Dikkan Abin Da Ya Zo Da Shi, Muna Kafirta Wanda Yaqi Hakan Kuma Muna Yaqarsa.

Bayan Haka: Allah Ya Aiko Da Gaskiya Zuwa Ga Bayinsa Yana Mai Basu Sako Na Bushara Da Tsoratarwa, …

[[Cigaba]] FASSARAN LITTAFIN HUQBATUN MINAT TARIKH RUBUTU NA 12

Image
Cigaba Da Fassarar Littafin (حقبة من التاريخ)

Rubutu Na 012

Idan Masu Karatu Basu Mantaba Wancan Satin Da Ya Gabata Mun Tsayane A Shafi Na 42 Inda Yanzu Kuma Zamu 'Dora Zuwa Shafi Na 44 Idan Allah Ya Amince Mana.

NA'AM MALAM YACE:
Yaqar Wadanda Suka Bar Musulunci Da Wadanda Suka Hana Zakka:

Abubakar Ya Kulla -Damarar Yaqar Wadanda Suka Bar Musulunci Da Wadanda Suka Hana Zakka, Haqiqa Sahabbai Sunyi Magana Tare Da Siddiq Gameda Wannan, Sukace Kada Ya Yaqi Wadannan Da Suka Bar Musulunci, Saboda Tsoron Abin Da Zai Faru Cikin Madina Da Ma'abota Cikinta Sai Yaqi, Sukayi Masa Magana Akan Ya Kyale Wadanda Suka Hana Zakka Da Abin Da Suke Kai Na Hana Zakkar Ya Bisu A Hankali, Har Imani Yayi Qarfi Cikin Zukatansu, Sannan Bayan Haka Su Zasu Bayar Da Zakka, Sai Abubakar Yace A'a, Ya Qi.

Daga Abu Huraira Yace: Umar Yacewa Abubakar Yaya Zaka Yaqi Mutane Alhali Annabi (S) Yace: An Umarceni Na Yaqi Mutane Harsai Sunce Babu Abin Bauta Bisa Cancanta Da Gaskiya Sai Allah, Kuma Muhammad M…