[[Cigaba]] FASSARAN LITTAFIN HUQBATUN MINAT TARIKH RUBUTU NA 15

Cigaba Da Fassarar Littafin (حقبة من التاريخ)

Rubutu Na 014

Idan Ba'a Mantaba Har Yanzu Dai Muna Cikin Bayani Akan Khalifanci Abubakar (R) Wanda A Wancan Satin Da Ya Gabata Mun Tsayane A Shafi Na 48 Wanda Yanzu Kuma Insha Allahu Zamu 'Dora Zuwa Shafi Na 49.

MALAM YACE:

●Banu Hanifa Da Yaqin Yamama:

Abubakar (R) Ya Aika Khalid Bn Waleed Domin Yaqar Banu Hanifata, Haqiqa Abubakar (R) Gabanin Haka Ya Aika Ikhramatu Bn Abiy Jahal, Da Kuma Sharahbil Bn Hassanatu, Rundunar Abu Hanifa Sun Kasance Yawansu Yakai Kimanin Dubu Arb'ain ( 40,000 ) Da Khalid Yaje Sai Ya Sanya Sharahbil Shine Na Gaba Na Dama Shine Zaid Bnul Khaddab Da Al-Maisarata Abaa Huzaifata.

Musulmai Sukayi Gaba, Har Khalid Ya Sauka Da Su Kan Wani Tudun Yashi, Yana Ganin Garin Yamama, Kamar Yana Gani, Sai Ya Kafa Rundunarsa, Tutar Muhajirai Tana Tare Da Salim Bawan Abu Huzaifata, Tutar Mutanan Madina Tana Wajen Thabit Bn Qaiys, Yaqi Yayi Tsanani, Har Thabit Ya Haqawa Diddigensa Rami Izuwa Rabin Kwaurinsa, Bayan Yasanya Lakafani Ya Sanya Turare, Bai Gusheba Har Sai Da Aka Kasheshi, Sai Wasu Mutanan Makka Sukace Da Saalim Bawan Abu Huzaifa: Kana Tsoron A Kawo Mana Farmaki A Karyamu Ta 6angaranka?

Sai Yace Idan Kuwa Akayi Haka Tir Da Ni Mahaddacin Al-Qur'ani, Khalid Bn Walid Ya Kawo 'Dauki (Da Makami) Ya Kewaya Har Ya Dawo, Sannan Ya Zo Ya Shuga Tsakiyar Musulmai Da Kafirai, Sai Yayi Kira A Fito, Sai Ya Kasance Babu Wanda Zai Fito Sai Ya Kasheshi, Da Yaqi Yayi Tsanani Sai Ya Ware Muhajirai Daban Ya Ware Ansarawa Daban, Larabawa Daban, Sannan Ya Sanya Musu Jagorori, Har Mutane Su Iya Gane Cewa Ta Ina Sakaci Zai Zo.

Musulmai Sukayi Haqurin Da Ba'a Ta6a Ganin Irinsa Ba, Basu Gushe Ba Suna Tunkarar Abokan Gabarsu, Har Allah Yayi Musu Budi, Kafirai Suka Juya Suka Gudu Suka Shige Wani Lambu (Kewayayye Da Ake Kiransa Ginin Mutuwa) Sai Suka Rufe Shingen Sahabbai Suka Kewayeshi,

Sai Barra'u Ibn Malik Yace: "Ya Ku Taron Musulmi.! Ku Jefani Cikin Kewayen, Sai Suka 'Dauki Garkuwa Suka Sakashi A Ciki Suka 'Dagata Har Sai Da Suka Jefashi Ta Saman Katanga, Bai Gushe Ba Yana Yaqarsu Zuwa Ga Qofarta Har Sai Da Ya Budeta, Daganan Musulmai Suka Riqa Shiga Ta Katanga Ta Kofa, Suna Kashe Wadanda Sukayi Ridda Daga Cikin Mutanan Yamama, Har Sai Da Suka Riski Gurin Da Musailamatu Yake, Sai Wahashi Ibn Harbin Yayi Gaba Ya Jefeshi Da Mashinsa Ya Sameshi Ya Kasheshi,
(Wahshi Yana Cewa: "Na Kashe Mutumin Da Ya Fi Kowa Alheri Cikin Mutane A Jahiliyya, Da Mafi Sharrin Mutane Cikin Musulunci).

Adadin Wadanda Aka Kashe Sunkai Mutum Dubu Goma (10,000) Ankashe Musulmai Mutun Dari Shida, Sauran Suka Shiga Cikin Ganuwa, Sai Khalid Yayi Sulhu Da Su, Ya Kirasu Zuwa Ga Musulunci, Dukkansu Suka Sallama, A Cikinsu Akwai Matar Nan Wadda Aliyi Bn Abiy 'Dalib Yayi Sadaka Da Ita, (Kaula Bnt Jafa'ar Bn Qais) Ta Haifa Masa 'Da Muhammad Wanda Akecemasa Muhammadu 'Dan Hanafiyya.

Muhadu A Rubutu Na 15 in shaa Allah.

Wassalamu Alaikum Warahamatullah.

Littafin: Dr Uthman bin Muhammad Alkhamis

Fassarawa: Asheer Abdallah Muh'd Sani Kano

Gyarawa/Gabatarwa: Muhammad Khalid Alfallatee

Comments

Popular posts from this blog

BUHARI APPOINTS ADAMU NEW IGP

[[Siyasar Kano]] HAKIKANIN ABINDA YAFARU YAU A HUKUMAR HIZBAH

[[Ran maza ya bace]] DUK WANDA YA SACI AKWATIN ZABE ABAKIN RANSA!!