[[Labarai]] CP WAKILI YA KAIWA SHUGABAN IZALAN KANO ZIYARA!

CP MUHAMMAD WAKILI YA KAIWA SHUGABAN IZALA NA JIHAR KANO ZIYARA.

A yau Asabar, 16-3-2019 ne, Kwamishinan ÿan Sanda na Jihar Kano Muhammad wakili ya kai ziyarar ga shugaban Kungiyar Izala na jihar Kano, Dr. Abdullahi Saleh Pakistan.

CP wakili, ya kai wannan ziyara ne domin girmamawa da kuma samun kwarin gwiwa a ayyukan da yake gabatarwa a wannan jiha tamu mai albarka.

A yayin ziyayar, Dr. Abdullahi Saleh Pakistan ne ya fara gabatar da jawabai na nasiha da jan hankali ga Cp wakili akan ya rike aikinsa hannu biyu-biyu, kuma yasan cewa Allah zai tambayeshi akan dukkan abinda ya gabatar.

" ka sani cewar dukkan aikin da mutum yakeyi, zai iya wakiltar musulunci a wajen, kayi iyaka kokarinka wajen kare musulinci da aikin da kakeyi. Kuma kayi Adalci a aikinka, domin Allah zai tsayar dakai yayi maka hisabi a kiyama...''
- Inji Dr. Pakistan

Dr. Abdulmudallib Muhammad, shima ya dora da nasiha ga CP wakilin, duk dai don fita hakkin shari'a akansa.

Shima a nasa bangaren, Cp Wakili yace yaji dadin nasihun da malaman suka gabatar masa, inda yace, dama yana bukatar nasiha domin ya samu kwarin gwiwa a inda yake yin daidai, ya kuma gyara inda yake da kusakurai.

''Ni bana siyasa, bani da Jam'iyya, kuma bazan siyar da lahirata akan duniyata ba, balle na siyar da lahirata akan duniyar wani, kunga babbar asara kenan...''
- Inji CP Waliki.

CP wakili ya bukaci malaman Kungiyar Izala, su tayashi addu'a domin dacewa a aikinsa, sannan ya bukaci a koyaushe idan yayi kuskure to a gyara masa.

"in nayi abinda ba daidai ba, ku kirani a waya ku gyara min, ko ku aika min da sako, ko kuzo, ko ku aiko ni nazo" Inji Wakili.

A karshe, Dr. Pakistan ya gabatar da kyautar Alqur'ani mai girma, da littattafai na addinin musulunci da Kwamishinan ÿan sandan na Kano.

A madadin Jagororin kungiyar Izala a matakin jiha, muna fatan alkhairi ga kwamishina, kuma muna rokon Allah ya bashi ikon yin adalci tsakanin al'umma.
Daga:
Awaisu Al'arabee Fagge.
Director, JSM Kano State.
16-3-2019

Comments

Popular posts from this blog

BUHARI APPOINTS ADAMU NEW IGP

[[Siyasar Kano]] HAKIKANIN ABINDA YAFARU YAU A HUKUMAR HIZBAH

[[Ran maza ya bace]] DUK WANDA YA SACI AKWATIN ZABE ABAKIN RANSA!!