[[Tausayi]] TAUSAYIN SAYYIDINA USMAN (R) GA TALAKAWAN MADINA!

A wata shekara aka yi wani mummunan fari, abinci ya yi matukar wahala ga mutanen Madina. Ko da kuɗi sai an sha wahala kafin a samu abinda za'a ci.

Ana cikin wannan yanayi, tsanani ya yi tsanani, kwatsam sai ga wasu raƙumma kimanin guda dari ko fiye da haka sun iso Madina daga ƙasar Sham (Syria) ɗauke da lodin kayan abinci da hatsi masu yawan gaske, kuma duk mallakin Sayyidina Usmanu dan Affan ne (RA).

Koda zuwan waɗannan raƙuma, sai 'yan kasuwa da yawa suka zagaye Sayyidina Usmanu suna so su saya waɗannan kaya. Sai ya tambaye su wacce riba zasu ba shi? Suka ce za su ba shi riba kashi biyar bisa ɗari. Ya ce, a'a, ai akwai wanda zai bashi fiye da haka.

Sai suka yi mamaki, wane ne wanda zai iya ɗora masa akan yadda suka taya? Su dai basu san wani ɗan kasuwa ba wanda zai iya ƙara masa akan haka ba.

Sai yace dasu, "Ni kuwa na san wani wanda zai bani riba linki ɗari bakwai akan kowanne dirhami guda!" Sai ya karanta masu wata aya daga cikin Qur'ani wadda Allah Maɗaukaki Ya ambaci wannan riba, inda Yake cewa:

مَثَلُ الَّذِينَ يُنْفِقُونَ أَمْوَالَهُمْ فِي سَبِيلِ اللَّهِ كَمَثَلِ حَبَّةٍ أَنْبَتَتْ سَبْعَ سَنَابِلَ فِي كُلِّ سُنْبُلَةٍ مِائَةُ حَبَّةٍ وَاللَّهُ يُضَاعِفُ لِمَنْ يَشَاءُ وَاللَّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ

"Misalin waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu a cikin hanyar Allah, kamar misalin ƙwãyã ce (ta hatsi) wadda ta tsirar da zangarniya bakwai, a cikin kõwace zangarniya akwai ƙwãya ɗari. Kuma Allah Yana riɓanyawa ga wanda Ya so. Kuma Allah Mawadãci ne, Masani." (Baƙarah: 2: 261)

Sai ya ɗora da cewa, "Ya ku 'yan kasuwa, ku shaida cewa, na bayar da dukkan wannan ga talakawan Madina!"

Allahu Akbar!

Ina Attajirai? Ina 'yan Kasuwa? Mu sani cewa duk abinda muka bayar saboda Allah shine namu, wanda kuma muka ajiye a wajemmu ba namu bane, domin wata rana zai zama gado ga wasummu. Ku zo mu yi koyi da Annabi ﷺ da Sahabbansa waɗanda Allah Ya yarda dasu, ta hanyar taimakon mabuƙata daga al'umma, a cikin wannan wata mai alfarma na Rajab, da Sha'aban da Watan Ramadan masu zuwa.

Allah Ka ba mu zuciyar taimaka wa al'ummar Annabi ﷺ, Amin.
.

Comments

Popular posts from this blog

BUHARI APPOINTS ADAMU NEW IGP

[[Siyasar Kano]] HAKIKANIN ABINDA YAFARU YAU A HUKUMAR HIZBAH

[[Ran maza ya bace]] DUK WANDA YA SACI AKWATIN ZABE ABAKIN RANSA!!