Posts

Showing posts from April, 2019

[[Tsautsayi]] ABINDA YA FARU DA ZAINAB HABIB ALIYU

Image
Abinda yafaru da zainab Habib Aliyu!!

Zainab;
Yarinya ce da tayi tafiya zuwa Saudi Arabia,
da niyyan yin aikin Umura,
Sun samu sauka lafiya ita da yan uwanta,
suka bar jiddah
Zuwa Madina,
Har sun isa Madina suna zaune ita da mahaifiyar ta
a hotel,
Kawai sai ga yan sanda suka zo suna nemanta
Nantake suka tafi da ita,
Sai daga baya
Ta kira mamar a waya tafada mata cewa tana prison,

Wai ashe an samu wani daurin kaya da akayi tagging sunanta akai,
Kuma qwayoyin tramadol ne Aciki masu hadari!
Kuma abin takaici shine
Ita jakarta guda daya ce kawai,
Ashe wasu ma'aikanta (marasa tsoron Allah) da suke aiki a filin jirgin sama na Aminu Kano da suka ga Cewa bata da kaya da yawa
Shine suka daura mata wannan qarin jakar da sunanta alhali Ita bata sani ba!
Shiyasa lokacinda ta sauka
Taje wajen daukan kaya,
Kayanta yana Hawa belt sai ta dauko ta fito abinta,
saboda ita kwata kwata batasanma da akwai wani kaya da akasa da sunanta ba,
To su jamian yan sanda da sukaga kaya
Yarage kuma gashi duk fa…

[[Cigaba]] FASSARAN LITTAFIN HUQBATUN MINAT TARIKH RUBUTU NA 015B

Image
CIGABA DA FASSARAR LITTAFIN (حقبة من التاريخ)

RUBUTU NA 015B

Malam Yace:

Mahaan (Jagoran Rumawa) Ya Nemi Ya Gana Da Khaleed Bn Waleed, Sai Khaleed Ya Fita Ya Sameshi Sai Mahaan Yace: "Mun Samu Labarinku Cewa Abin Da Ya Fito Da Ku Daga Garuruwanku Yunwace Da Wahala, Ku Zo Wajena Kowanne Daga Cikinku Zan Bashi Dinare Goma Da Kayan Sawa Da Abinci, Ku Koma Garuruwanku Kuje Ku Zauna, Yayin Da Shekara Ta Zagayo Sai Mu Qara Aika Muku Kwatankwacinsa.

Sai Khaleed (Saboda Ya Tsoratar Da Shi) Yace; Lallai Mu Bamu Fito Daga Garinmu Ba Saboda Abin Da Ka Ambata Sai Dai Mu Mutanene Masu Shan Jini, Kuma Labari Ya Ishe Mu Cewa Babu Jinin Da Yafi Dadi Irin Jinin Mutanan Rumawa Saboda Haka Muka Zo.

Sannan Suka Rabu Wandannan Jarimai Suka Buga, Suka Kewaya Cikin Yaqi Ya Tsaya Akan Qafafunsa, (Ya Kankama) Rumawa Da Sukazo Suna 'Daga Kurus 'Dinsu Suna Wani Sauti Mai Tsoratarwa Kamar Tsawa, Malamansu Da Shugabanninsu Suna Ta Kwadaitar Da Na Qasansu Akan Yaqin, Suna Cikin Yawa Da Tanadi Wanda Ba…

[[Cigaba]] FASSARAN LITTAFIN HUQBATUN MINAT TARIKH RUBUTU NA 015A

Image
CIGABA DA FASSARAR LITTAFIN (حقبة من التاريخ)

RUBUTU NA 015A

Idan Mai Karatu Bai Manta Ba Mun Tsayane A Shafi Na 50 Inda Yanzu Kuma Zamu 'Dora Izuwa Shafi Na 52 Idan Allah Ya Amince.

Na'am! Malam Yace:

-Yazid Bn Abiy Sufyan Tare Dashi Da Mutane Da Yawa, Ya Turashi Dumashka. -Abiy Ubaidata Bn Jarrah Ya Turashi Hims, -Amru Bnul Aass Sai Ya Turashi Palasdinu. Sannan Daga Baya Ya Aika Da Qarin Mutane Ga Tawagar Yazid Bn Abiy Sufyan Da Sharahbil, Ya Kuma Sake Aika Ikhrama Ubn Abiy Jahal.

■Wadanda Suka Taru Sukaje Yaqin Yarmuk Daga Cikin Manya Manyan Sahabbai:

Abu Ubaida Bn Jarrah, Zubair Bn Awwaam, Abdullahi Bn Mas'ud, Abud Dardaa, Abu Huraira, Sharahbil Bn Hassana, Amru Bn Aass, Abu Sufyan Bn Harbin, Yazid Bn Abiy Sufyan, Ikramatu Bn Jahl.

Adadin Tawagar Musulmai Sun Kai Kimanin Dubu Ashirin Da Bakwai ( 27000) Su Kuma Adadin Rundunar Kafirai Sun Kai Dubu Dari Da Ashirin (120000) Sannan Sugabannin Tawagogi Suka Aika Ga Abubakar Suna Sanar Da Shi Abin Da Ya Faru Na Al'amura …