[[Cigaba]] FASSARAN LITTAFIN HUQBATUN MINAT TARIKH RUBUTU NA 015A

CIGABA DA FASSARAR LITTAFIN (حقبة من التاريخ)

RUBUTU NA 015A

Idan Mai Karatu Bai Manta Ba Mun Tsayane A Shafi Na 50 Inda Yanzu Kuma Zamu 'Dora Izuwa Shafi Na 52 Idan Allah Ya Amince.

Na'am! Malam Yace:

-Yazid Bn Abiy Sufyan Tare Dashi Da Mutane Da Yawa, Ya Turashi Dumashka. -Abiy Ubaidata Bn Jarrah Ya Turashi Hims, -Amru Bnul Aass Sai Ya Turashi Palasdinu. Sannan Daga Baya Ya Aika Da Qarin Mutane Ga Tawagar Yazid Bn Abiy Sufyan Da Sharahbil, Ya Kuma Sake Aika Ikhrama Ubn Abiy Jahal.

■Wadanda Suka Taru Sukaje Yaqin Yarmuk Daga Cikin Manya Manyan Sahabbai:

Abu Ubaida Bn Jarrah, Zubair Bn Awwaam, Abdullahi Bn Mas'ud, Abud Dardaa, Abu Huraira, Sharahbil Bn Hassana, Amru Bn Aass, Abu Sufyan Bn Harbin, Yazid Bn Abiy Sufyan, Ikramatu Bn Jahl.

Adadin Tawagar Musulmai Sun Kai Kimanin Dubu Ashirin Da Bakwai ( 27000) Su Kuma Adadin Rundunar Kafirai Sun Kai Dubu Dari Da Ashirin (120000) Sannan Sugabannin Tawagogi Suka Aika Ga Abubakar Suna Sanar Da Shi Abin Da Ya Faru Na Al'amura Mai Girma, Suka Nemi Ya Qara Mayaqa, Sai Abubakar Ya Rubuta Musu Akan Su Hadu Su Zama Runduna Guda, Ku Matai Maka Addinin Allah Ne, Kuma Allah Ya Taimakon Wanda Duk Ya Taimaki Addininsa, Kuma Allah Ya Tozarta Wanda Ya Kafirce Masa, Qaranci Ba Zaisa A Karyaku Ba Irin Ku Ba, Sai Dai A Karyaku Daga Zunuban Da Za Ku Aikata Saboda Haka Ku Kiyaye Shi.

Sannan Abubakar As-Siddiq Yace: "Zan Shagaltar Da Kafirai Daga Wasu-Wasin Shedan Da Khalid Bn Waleed, Sai Ya Aika Masa daga Iraqi, Yace Ya Taho Garin Sham Shida Jama'arsa, Idan Iso Sham Shine Shugaban Dukkanninsu, Khalid Sai Ya Sanya MUSANNA BN HARISLA Ya Zama Shine Wakilinsa Ya Fuskanci Garin Sham Yana Mai Sauri Tare Da Runduna Dubu Tara Da 'Dari Biyar (9500) Ya Bi Wasu Hanyoyin Da Gabaninsa Babu Wanda Ya Bisu Saboda Ya Rage Hanya, Ya Keta Tudu Da Kwarin Dajika Ya Wuce, Ya Yanyanke Kwarirrika, Ya 'Dauki Me Nuna Masa Hanya Shine Nafi'u Bn Umairata Dhaa'iriy.

Ta Kasance Qasa Mai Qarancin Ruwa, Yayin Da Suka Rasa Ruwa, Sai Suka Yanka Raquma, Abin Da Ke Cikin Raquman Sai Suka Bawa Dokunansu Suka Sha, Ya Isa A Cikin Kwanaki Biyar, Wani Cikinsu Masanin Larabawa Ya Gayawa (Khaleed) Cewa Idan A Cikin Rana Kaza Ta Zama Kana Bishiya Kaza A Rana Kaza Kai Da Wadanda Kuke Tare Kun Tsira, Idan Kuwa Baku Kai Ba Har Rana Kaza To Zaka Halaka Kai Da Wanda Suke Tare Da Kai, Sai Suka Wayi Gari A Wurin, Sai Khaleed Yace: "Wayewar Gari Mutane Zasu Yaba Da Tafiyar Dare, Sai Ya Zama Karin Magana.

Sai Wani Daga Cikin Larabawa Ya Fita Yana Bincike Akan Lammuran Sahabbai, Sai Yake Cewa Ai Naga Wasu Mutane Masu Yawan Bauta Ne Cikin Dare, Da Rana Kuma Mahaya Ne (Jarumai), Na Rantse Da Allah Da Shugabansu Zaiyi Sata Da Sun Yanke Masa Hannu, Ko Yayi Zina Da Sun Jefeshi, Sai Jagoran Romawa Yace Masa; Na Rantse Da Allah Idan Gaskiya Ka Fada Cikin Qasa Ya Fiyemin Alheri Akan Bayanta. (Ma'ana: Sunfi Qarfin Mu).

Yayin Da Khaleed Yazo Daga Iraq Sai Wani Mutun Cikin Larabawa Ya Gamu Da Khaleed Yake Ce Masa; Kaga Kuwa Yawan Rumawa Gaku Kuma 'Yan Kadan, Sai Khaleed Yace: Kaicon Ka! Shin Kana Tsoratar Da Ni Rumawa Ne? Ai Runduna Tana Zama Da Yawane Yayin Da Taci Nasara, Yana Kuma Zama 'Yar Kadan Idan Aka Ta6ar Da Ita Ba Wai Yawan Mazaje Ba, Nayi Burin Inama Dokina Al-Asqar Ya Warke Daga Ciwon Da Yake Tare Da Shi Kuma Ace Sun Ninka Adadin Da Suke Yanzu.

Jagoran Rumawa ya nemi yagana da khaleed Muhadu A Rubutu Na 15B domin ganin yadda ganawarsu din tawakana, tareda cigaba Har zuwa karshen khalifancin sayyidina Abubakar (R.A).

Wassalamu Alaikum Warahamatullah.

Littafin: Dr Uthman bin Muhammad Alkhamis

Fassarawa: Ashiru Abdullah Muh'd Sani kano

Gyarawa/Gabatarwa: Muhammad Khalid Alfallatee

Comments

Popular posts from this blog

BUHARI APPOINTS ADAMU NEW IGP

[[Siyasar Kano]] HAKIKANIN ABINDA YAFARU YAU A HUKUMAR HIZBAH

[[Ran maza ya bace]] DUK WANDA YA SACI AKWATIN ZABE ABAKIN RANSA!!