[[Cigaba]] FASSARAN LITTAFIN HUQBATUN MINAT TARIKH RUBUTU NA 015B

CIGABA DA FASSARAR LITTAFIN (حقبة من التاريخ)

RUBUTU NA 015B

Malam Yace:

Mahaan (Jagoran Rumawa) Ya Nemi Ya Gana Da Khaleed Bn Waleed, Sai Khaleed Ya Fita Ya Sameshi Sai Mahaan Yace: "Mun Samu Labarinku Cewa Abin Da Ya Fito Da Ku Daga Garuruwanku Yunwace Da Wahala, Ku Zo Wajena Kowanne Daga Cikinku Zan Bashi Dinare Goma Da Kayan Sawa Da Abinci, Ku Koma Garuruwanku Kuje Ku Zauna, Yayin Da Shekara Ta Zagayo Sai Mu Qara Aika Muku Kwatankwacinsa.

Sai Khaleed (Saboda Ya Tsoratar Da Shi) Yace; Lallai Mu Bamu Fito Daga Garinmu Ba Saboda Abin Da Ka Ambata Sai Dai Mu Mutanene Masu Shan Jini, Kuma Labari Ya Ishe Mu Cewa Babu Jinin Da Yafi Dadi Irin Jinin Mutanan Rumawa Saboda Haka Muka Zo.

Sannan Suka Rabu Wandannan Jarimai Suka Buga, Suka Kewaya Cikin Yaqi Ya Tsaya Akan Qafafunsa, (Ya Kankama) Rumawa Da Sukazo Suna 'Daga Kurus 'Dinsu Suna Wani Sauti Mai Tsoratarwa Kamar Tsawa, Malamansu Da Shugabanninsu Suna Ta Kwadaitar Da Na Qasansu Akan Yaqin, Suna Cikin Yawa Da Tanadi Wanda Ba'a Ta6a Ganinsa Ba, Su Kuwa Musulmai Suka Hau Kansu Karo 'Daya Sai Su Dare Suka Gudu Yaqi Ya Qare Da Kyakkyawar Nasara Ga Musulmai.

Wasu Abubuwa Da Suka Faru Na Jarintaka:

Ikrima Bn Abu Jahal Ya Tsaya A Ranar Yarmuk, Yace Na Yaqi Manzon Allah (S) A Wasu Gurare Yau Kuma Na Gudu? Sai Yayi Kira Yace; Waye Zaiyi Mubaya'a Sai (Baffashi) Haris Ibn Hisham Yayi Masa Mubaya'a Da Dirar Bn Azwad Da Mutum Dari Hudu Daga Cikin Mahaya Na Musulmai, Sukayi Yaqi Mai Tsanani Har Aka Kashe Da Yawa Daga Cikinsu.

Haqiqa Malaman Tarihi Sun Ambata,  Yayin Da Aka Kayar Da Su Sai Sukace Abasu Ruwa Su Sha, Sai Aka Zo Musu Da 'Dan Ruwa, Sai Kowa Ya Riqa Fifita 'Dan Uwansa Akansa, Har Sai Da Dukkansu Suka Mutu Babu Wanda Yasha Daga Cikinsu. Musulmai Suka Kama Gurin Bautar Muhanna Suka Rabashi Gida Biyu, Rabi Suka Sanyashi Ya Koma Masallaci, 'Dayan Kuma Suka Barshi A Yadda Yake Masallacin A Yanzu Ana Kiransa Da Masallacin Dimashqa.

《》 《》 《》 《》 《》

Wannan Shine Qarshen Abin Da Ya Wakana Cikin 'Dan Takurararran Bayani Akan Khalifancin Sayyidina Abubakar As-Siddiq Allah Ta'alah Ya Qara Yarda A Gareshi Ya Sadar Da Mu Cikin Albarkarsa.

ANNAN ZAMU TSAYA SAI KUMA KUMA A RUBUTU NA 016 IDAN ALLAH YASO INDA ZAMU SHIGA CIKIN TAQAITACCEN TARIHIN ABIN DA YA WAKANA A ZAMANIN KHALIFANCIN BABBAN SAHABI UMAR BN KHADDAB (RA).


Wassalamu Alaikum Warahamatullah.

Littafin: Dr Uthman bin Muhammad Alkhamis

Fassarawa: Ashiru Abdullah Muh'd Sani kano

Gyarawa/Gabatarwa: Muhammad Khalid Alfallatee

Comments

Popular posts from this blog

BUHARI APPOINTS ADAMU NEW IGP

[[Siyasar Kano]] HAKIKANIN ABINDA YAFARU YAU A HUKUMAR HIZBAH

[[Ran maza ya bace]] DUK WANDA YA SACI AKWATIN ZABE ABAKIN RANSA!!