[[Tsautsayi]] ABINDA YA FARU DA ZAINAB HABIB ALIYU

Abinda yafaru da zainab Habib Aliyu!!

Zainab;
Yarinya ce da tayi tafiya zuwa Saudi Arabia,
da niyyan yin aikin Umura,
Sun samu sauka lafiya ita da yan uwanta,
suka bar jiddah
Zuwa Madina,
Har sun isa Madina suna zaune ita da mahaifiyar ta
a hotel,
Kawai sai ga yan sanda suka zo suna nemanta
Nantake suka tafi da ita,
Sai daga baya
Ta kira mamar a waya tafada mata cewa tana prison,

Wai ashe an samu wani daurin kaya da akayi tagging sunanta akai,
Kuma qwayoyin tramadol ne Aciki masu hadari!
Kuma abin takaici shine
Ita jakarta guda daya ce kawai,
Ashe wasu ma'aikanta (marasa tsoron Allah) da suke aiki a filin jirgin sama na Aminu Kano da suka ga Cewa bata da kaya da yawa
Shine suka daura mata wannan qarin jakar da sunanta alhali Ita bata sani ba!
Shiyasa lokacinda ta sauka
Taje wajen daukan kaya,
Kayanta yana Hawa belt sai ta dauko ta fito abinta,
saboda ita kwata kwata batasanma da akwai wani kaya da akasa da sunanta ba,
To su jamian yan sanda da sukaga kaya
Yarage kuma gashi duk fasinjoji sun wuce
Sai suka dauke shi zasu duba,
In babu kayan laifi,  sai su jira maishi
Inya tuno yazo ya karbi kayansa,
Ashe qwayoyin ne cike a ciki,
Nan danan sukabi diddiginta har Madina, sukaje suka kamata,
Wanda wallahi yanxu
Inba sa'aba tana fuskantar hukumcin kisa!!
Dukda dai mahaifinta yaje airport din take yafada masu cewa suyi bincike don dorawa yarsa akayi amma ba kayanta bane!!

To alhamdu lillah,
an Kama mutane shida kuma maikatan wajen wadanda  sune suka dora mata kayan,!

Ashe kenan wannan bashine Karon farko ba,
Sun dade kenan sunayin hakan,
Mafiya yawan wadanda ake kashewa da sunan irin wannan laifin wallahi tayiwu bamasu laifi bane!

Yakamata a taimaka aceto rayuwar wannan yarinyar!!
Musamman ambassadon Nigeria yakamata yasa baki acikin wannan halin don  a kubutarda wannan baiwar Allah!!
Sarakuna da gwamnoni yakamata suma su sanya baki!!

Allah ya kubutarda ita,
Allah ya karemu da yan'uwanmu daga fadawa irin wannan ibtila'iyin

Comments

Popular posts from this blog

BUHARI APPOINTS ADAMU NEW IGP

[[Siyasar Kano]] HAKIKANIN ABINDA YAFARU YAU A HUKUMAR HIZBAH

[[Ran maza ya bace]] DUK WANDA YA SACI AKWATIN ZABE ABAKIN RANSA!!