[[BATUN RUGA]] QUNGIYAR MATASAN AREWA TA BAIWA GWAMNATI DA GWAMNONIN KUDU KWANA 30

Munsamu wannan labarin Daga Aliyu Ahmad
Yake cewa:
Kungiyar Matasan Arewa ta baiwa gwamnatin tarayya da sauran gwamnonin da suka ki amincewa da tsarin samar da matsuguni ga Fulani makiyaya a yankunansu wa'adin wata guda su cimma matsaya ko kuma kungiyar ta dauki mataki kan 'yan kudu dake zaune a yankunan Arewa.

Kungiyar wadda kimanin shekaru biyu kenan da ta fitar da sanarwar fatattakar kabilar Ibo daga yankunan Arewa biyo bayan barazanar da kungiyar IPOB karkashin jagorancin Nnamdi Kanu ta yi a shirin ta na kafa yankin Biafra, ta sanar da hakan ne a yau Laraba a Abuja a yayin taron manema labarai da ta gayyata.

Kungiyar ta kara da cewa ta yi mamakin yadda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da manyan 'yan kudu irin su, Bola Tinubu, Olusegun Obasanjo, Fani Kayode da kungiyoyin yankunan irin su Ohaneze, Afenifere da suke adawa tsarin na samawa Fulani makiyaya matsuguni.

Kungiyar ta ce ya kamata mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya yi murabus saboda ba ya tare da ayyukan gwamnati musamman adawar da ya nuna kan samar da ruga ga makiyaya.

A yayin da yake jawabi, shugaban kungiyar, Abdulaziz Suleiman, ya kara da cewa sun yi mamakin yadda wasu daga cikin gwamnonin kudu da shugabannin su suke cin mutuncin manyan arewa da shugabannin addini ciki har da su Mujadaddi Sheh├╣ Usman Danfodio, duk don saboda shirin da gwamnati ke shirin fitarwa na samawa Fulani makiyaya guri.

"Mun baiwa gwamnatin tarayya da gwamnonin yankin kudu wa'adin kwana talatin su cimma matsaya ko kuma mu dauki mataki, kuma babu gudu babu ja da baya", crwar kungiyar.

Kungiyar ta kara da cewa an gina fitintinu iri-iri a yankunan Arewa duk don saboda a rusawa al'ummar Arewa tattalin arziki. Kuma ba komai ya jawo hakan ba sai don yadda aka saka addinnanci da siyasa a kasar nan.

Kungiyar ta kuma yi kira da shugabannin yankunan kudu da kungiyoyin su da su kiyayi ci  zarafin iyaye da kakannin al'umar yankin arewa domin cin zarafin ya yi yawa.

Kungiyar ta kara da cewa al'ummar arewa ba su da jagora nagari, saidai 'yan siyasa wadanda kawai bukatar su ce take hada su da talakawa, amma ba wani abu ci gaban su ba.

Kungiyar ta kara da cewa idan har ba su tashi tsaye sun yaki matsalar nan ba, na gaba dan arewa saidai ya zama dan kallo a kasar nan.

"Dan Arewa kamar kyandir yake, inda ake kunna masa wuta yana narkewa wasu kuma suna amfana da haskensa.

"Yanzu bari na ba ku misali, idan ka shiga bankunan dake yankunan Arewa za ka kashi 70 duk mutanen kudu ne ma'aikatan su, yayin da kuma ga matasan arewa birjik sun kammala karatu babu aikin yi. To ya za a yi ba za a samu matsala a arewa ba", cewar kungiyar.

Comments

Popular posts from this blog

BUHARI APPOINTS ADAMU NEW IGP

[[Siyasar Kano]] HAKIKANIN ABINDA YAFARU YAU A HUKUMAR HIZBAH

[[Ran maza ya bace]] DUK WANDA YA SACI AKWATIN ZABE ABAKIN RANSA!!